Shugaban hukumar Ibrahim Inga ya bayyana a jiya cewa, daga cikin mutane 11 da suka mutu, gawarwakin mutane 8 kawai aka gano.
Ibrahim Inga ya shaidawa manema labarai cewa, ambaliyar ta lalata gidaje 90, kuma a kalla mutane 500 ne ta raba da gidajensu.
Ya ce gwamnati na shirya sansanonin wucin gadi domin tsugunar da wadanda suka rasa matsugunansu.
Ambaliyar dai ta shafi galibin mutanen da suka gina gidajen a kusa da bakin kogi a Suleja,yankin da ake samun hada-hadar jama'a sosai.
Makonni 6 da suka wuce, hukumar kula da yanayi ta kasar, ta mika gargadin aukuwar ambaliya a Lagos, da sauran biranen dake kusa da teku da ma wasu jihohi a fadin kasar dake yammacin Afrika. (Fa'iza Mustapha)