in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya za ta kafa hukumar kare hakkin dan adam mai zaman kanta
2017-07-10 10:20:24 cri

A ranar Lahadi kasar Somaliya ta kaddamar da kashin farko na shirin kafa hukumar kare hakkin adam mai zaman kanta ta kasar, wanda aka yi amanna cewar, muhimmin mataki ne da zai tabbatar da kare hakkin dan adam da ci gabansa.

Ministar kula da al'amurran mata da kare hakkin dan adam ta kasar Deqa Yasin, ta bayyana cewa, duk da irin kalubalolin da kasar Somaliya ke fuskanta, musamman matsalar tabarbarewar tsaro, talauci, da matsanancin fari, tabbatar da kafa hukumar kula da hakkin bil adama, wani muhimmin abu ne wanda za'a ba shi fifiko don ciyar da kasar gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China