in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaddamar a Rafah na kasar Masar
2017-07-09 12:08:04 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaddamar a garin Rafah na kasar Masar a ranar Jumma'a.

Cikin sanarwar, kasar Sudan ta yi Allah wadai da babbar murya game da harin ta'addancin da aka kaddamar a garin Rafah, wanda ya yi sanadiyyar kashe rayukan tare da jikkata wasu al'ummar kasar ta Masar.

Ma'aikatar harkokin wajen ta Sudan ta bayyana harin da cewa ya ci karo da dukkan dokoki da hakkokin dan Adam.

Kana gwamnatin Sudan ta aike ta sakon ta'aziyya ga gwamnatin kasar Masar da al'ummar kasar da kuma iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma jajantawa wadanda suka jikkata.

Sanarwar ta kuma nuna cikakken goyon bayanta ga kasar Masar game da dukkan matakan yaki da ta'addanci.

Tun da farko rundunar sojin Masar ta bada sanarwar cewa kimanin sojojin kasar 26 ne aka hallaka a lokacin harin wanda aka kaddamar a wajen binciken ababan hawa na sojojin kasar dake garin Rafah a arewacin Sinai, ta kara da cewa sojojin sun yi nasarar kashe maharan 40. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China