in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Sin sun cika shekaru 27 suna gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a ketare
2017-07-07 19:26:37 cri

Tabbatar da zaman lafiya yana daga cikin babban burin dan Adam. Sabo da wannan buri ne aka soma gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. Kasar Sin tana daga cikin zaunannun kasashe biyar na kwamitin sulhun MDD da suka aika sojojin kiyaye zaman lafiya mafiya yawa a ketare, kuma ya zuwa yanzu ta shafe shekaru 27 tana gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiye a ketare.

Wani jami'in ofishin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya ce, "sojoji da jami'an kiyaye zaman lafiya dake aiki a yankuna daban daban sun nuna siffar kasar Sin a matsayin babbar kasa mai tasowa dake kaunar zaman lafiya da kuma sauke nauyin dake kanta, kana sojojinta suna taka muhimmiyar rawa a fannin tabbatar da zaman lafiya a duniya."

Kasar Sin ta samu babban ci gaba a ayyukan kiyaye zaman lafiya da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi

A watan Afrilun shekarar 1990, a dangane da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, wannan shi ne karo na farko da aka bayar da wani labari game da sojojin kasar Sin, inda aka ce, masu sa ido guda biyar a fannin aikin soja daga sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin sun isa Damascus. Wannan bayanin da aka bayar tare da wasu rahotanni ya kasance shaidar kasar Sin na shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya a duniya. Ya zuwa yanzu, rundunar sojojin kasar Sin ta aika da masu aikin kiyaye zaman lafiya sama da dubu 35, wadanda suka gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya MDD guda 24, a sakamakon haka, kasashen duniya sun bayyana sojojin a matsayin ginshikin aikin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya'.

Aikin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ya samu ci gaba kwarai da gaske cikin shekaru 27 da suka gabata. Da farko, sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Sin sun yi aiki a yankin Gabas ta Tsakiya, kana yanzu haka suna fara gudanar da ayyuka a wurare daban daban a nahiyoyin Asiya da Afirka. Haka kuma, adadin sojojin da aka tura zuwa ketare ya karu daga guda 5 zuwa guda 2409, cikin har da, sojojin kasa, sojojn injiniya, sojoji masu aikin kiwon lafiya da dai sauransu, kana, wannan shi ne adadi mafi yawa a cikin zaunannun mambobin kwmaitin sulhu na MDD guda biyar. Wasu daga cikinsu kuma suna kan gaba wajen tura manyan hafsoshi, kwamanda da dai sauran masu matsakaitan mukami ko matsayi.

Bugu da kari, kudaden da kasar Sin ta samar a wannan aiki ya kasance na biyu cikin kasashen duniya, baya da bullo da tsarin ba da horaswa ga sojojin kiyaye zaman lafiya. Haka kuma, wasu sojojin kasar Sin sun tafi waje domin ba da darussa bisa gayyatar da MDD ta yi musu.

A watan Satumban shekarar 2015, a yayin taron kolin tattauna harkokin tabbatar da zaman lafiya a duniya da MDD ta shirya, gwamnatin kasar Sin ta shelanta cewa, za ta shiga shirin tura dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD. Sabili da haka, ta tsai da kudurin kafa wata zaunanniyar rundunar 'yan sanda ta tabbatar da zaman lafiya tare da wata rundunar sojin tabbatar da zaman lafiya mai kunshe da sojoji dubu 8. Sannan gwamnatin kasar Sin ta yi shelar cewa, za ta yi la'akari da bukatun MDD na aika karin ma'aikatan injiniya da jigilar kayayyaki da na jinya. A cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta horas da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya dubu 2 na sauran kasashen duniya, tare da kaddamar da shirye-shiryen kawar da nakiyoyi guda 10. Bugu da kari, a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta samar wa kungiyar AU taimakon soja da darajarsu za ta kai dalar Amurka miliyan dari 1, domin tallafawa kungiyar AU kafa wata zaunanniyar rundunar soja da rundunar ko-ta-kwana. Sannan, kasar Sin za ta taimakawa rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Afirka don kafa wani rukunin jiragen yaki masu saukar ungulu. Haka kuma, za a kebe wasu kudade daga asusun tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa na Sin da MDD ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya da MDD ke gudanarwa.

"Wadannan muhimman matakai ne da kasar Sin ta dauka domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk duniya, tare da sauke nauyin kasa da kasa dake bisa wuyanta. Sun kuma bayyana aniyar kasar Sin ta tabbatar da zaman lafiya da yadda kasar Sin take goyon bayan MDD wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin duniyarmu." Kamar yadda Wang Fan, mataimakin shugaban jami'ar koyon ilmin diflomasiyya ta kasar Sin ya bayyana. Yanzu, kasar Sin na hanzarta aiwatar da wadannan matakai kamar yadda ake fata. An yi hasashen cewa, za a shigar da sabbin matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk duniya sabo da kasar Sin ta yi kokarin nuna goyon baya da kuma halartar ayyukan tabbatar da zaman lafiya na MDD.

Sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suna tinkarar kalubaloli ba tare da jin tsoro ba

A ko da yaushe ana fuskantar hadari da kalubaloli a yankunan da ake gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya, wadanda suka hada da rikice-rikice, yunwa, talauci, yanayi mai zafi da cututtuka. Amma sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suna fuskantar irin wadannan kalubale ba tare da jin tsoro ko wata farfaba ba, lamarin da ya nuna jajurcewa na sojojin babbar kasa mai tasowa.

Daga shekarar 2014 zuwa 2015, an samu barkewar annobar Ebola a nahiyar Afirka. Duk da cewa, ana fuskantar hadarin yaduwar kwayoyin cutar, amma sojojin kasar Sin dake gudanar da ayyukan injiniya a kasar Laberiya ba su taba dakatar da ayyukansu ba, inda suka shafe kwanaki 28 suna gudanar da ayyukansu, kuma a kowace rana su kan yi aiki har na tsawon sa'o'i 16. Kana sun yi nasarar kammala aikin gina cibiyar jinyar wadanda suka kamu da cutar Ebola cikin kwanaki 30 kafin lokacin da aka kayyade.

Ban da haka kuma, a watan Maris na shekarar 2017, wani mummunan fada ya barke a garin Yei dake dab da kan iyakar kasar Sudan ta Kudu, inda aka yiwa wasu jami'an MDD 7 kawanya, wannan ya sa sun fuskanci barazana matuka. Sai dai bayan da sojojin kasar Sin masu kiyaye zaman lafiya a kasar suka samu wannan labarin, nan take suka tura wasu sojoji 12 domin ceton wadannan jami'an MDDr.

Bayan da sojojin kasar Sin suka fito daga sansanninsu, sun gamu da wasu mayakan da suke cikin motoci suna zuwa wurin da aka yi musayar wuta, wadanda suka rika harbi da bindigogi. Duk da cewa yanayin yana da matukar hadari, amma sojojin kasar Sin sun tinkari matsalar ba tare da jin tsoro ba. A karshe dai sun samu kai wadannan jami'an MDD cikin sasaninsu. Wannan aikin da sojojin kasar Sin suka gudanar cikin nasara sun samu yabo sosai daga tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu.

Har kullum sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata a wurare daban daban na fadin duniya, duk da cewa, su kan gamu da matsaloli masu tsanani, amma sun nunawa al'ummomin kasashen duniya kwarewarsu a fannin dandalin kiyaye zaman lafiya.

A lokacin zafi, yanayin zafin ya kan kai ma'aunin digiri 50 a kasar Mali, amma duk da haka sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun kammala aikin gina wani asibiti a cikin watanni hudu kawai. A kasar Kambodia kuwa, sun taba gina wata gada cikin yini daya kacal, lamarin da ya ba da mamaki matuka. Kana a birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, sojojin kiyaye zaman lafiyar da kasar Sin ta tura kasar a karon farko sun gina sabon sansani a wuri mai rairayi, amma sun kammala aikin cikin wata guda.

A cikin shekaru 27 da suka gabata, ayyukan da sojojin kasar Sin suka yi sun samu babban yabo daga wajen bangarori dabn daban, cibiyar nazarin zaman lafiyar kasa da kasa ta Stockholm ta kasar Sweden ta taba fitar da wani rahoto, inda aka bayyana sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin a matsayin fitattun sojoji mafiya kwarewar aiki a cikin daukacin takwarorinsu na MDD.

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da aikin kiyaye zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix shi ma ya bayyana cewa, ko shakka babu sojojin kasar Sin za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa a aikin kiyaye zaman lafiya na MDD kamar yadda suke yi yanzu.

Jama'a sun gamsu da gudummawar da sojojin kasar Sin suka bayar

A sabon halin da duniya ke ciki, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen martaba ra'ayin samar da makoma ta bai daya ga al'ummar duniya, a wani mataki na bude wani sabon babi a harkokin kiyaye zaman lafiya na kasar ta Sin. Yanzu ana kara samun sojojin kasar Sin wadanda ke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya, kuma jama'a sun gamsu sosai saboda irin sahihanci da kirki da kuma son zaman lafiya da sojojin kasar Sin suka nuna.

A kasar Mali dake yammacin nahiyar Afirka, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ba ma kawai sun kammala ayyukansu na yau da kullum ba, har ma sun yi kokarin samar da tallafin jin-kai, da gayyatar yara mazauna wurin don su shiga cikin sansanin kiyaye zaman lafiya, inda aka koya musu yare Sinanci gami da wakokin Sinanci, tare kuma da ba su kyautar kayayyakin karatu, domin kulla zumunci da al'ummar kasar ta Mali.

Hakika, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun nuna kauna da kulawa ga al'ummar kasashe daban-daban. Al'ummomin da sojojin ke gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban su kan kusanci sojojin kasar Sin, wadanda suka bayyana cewa, ko da yake ba su san kalmomin Turanci da aka rubuta a kayan sojojin ba, amma sun san cewa, wadannan sojojin kasar Sin ne, kuma mutane ne masu kirki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China