An bukaci gwamnatocin Afrika, su tabbatar da daidaiton jinsi a fannin ilimin kimiyya da fasaha domin samun ci gaba na bai daya.
Shugaban jami'ar aikin gona da fasaha ta Jomo Kenyatta dake Kenya Mabel Imbuga, ya ce matan Afrika kalilan ne ke aiki a bangaren kimiyya da fasaha idan aka kwatanta da maza a fadin nahiyar.
Ya ce al'adun Afrika na karfafa wariyar jinsin, lamarin da ke ragewa mata damar da suke da ita a fannin ilimi.
Mabel Imbuga na wannan jawabi ne a wajen taro kan inganta ilimin gaba da sakandare a fadin nahiyar.
Yayin taron da aka kammala a jiya Alhamis, mahalarta sun jadadda muhimmancin tabbatar da daidaiton jinsi a fannin ilimi domin cimma manufofin ajandar 2063.
A cewar mataimakin shugaban jami'ar Ibadan ta Nijeriya Abel Idowu Olayinka, ba maza da mata dama iri daya ta samun ilimi, zai zurfafa iliminsu. Yana mai cewa, hakan zai bunkasa tattalin arziki da zamantakewar nahiyar. (Fa'iza Mustapha)