in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari ga sojojin jamhuriyar Nijer
2017-07-06 11:10:03 cri
Bisa labarin da aka samu a jiya Laraba, wasu dakarun da ba a san inda suka fito ba sun kai hari ga wata rundunar sojojin gwamnatin jamhuriyar Nijer dake yammacin kasar, wanda ya haddasa rasuwar sojoji a kalla 6, yayin da wasu 2 suka jikkata.

Wannan rundunar sojoji sun kasance a wurin dake kusa da wani kauye a yankin Tassara dake yammacin kasar Nijer, inda suka gudanar da ayyukan hana fasa kwaurin miyagun kwayoyi.

A safiyar ranar 5 ga wata, wasu dakaru sun kai hari a sansanin rundunar.

An ruwaito hukumar tsaron kasar ta Nijer na cewa, dakarun sun gudu kuma sun yi awon gaba da motocin soji guda hudu. A halin yanzu, gwamnatin kasar ta dukufa don kama wadannan dakarun.

A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ya sanar da tsawaita dokar ta bace na tsawon watanni 3 a lardin Diffa dake kudancin kasar da kuma wasu larduna 6 dake yammacin kasar, domin fuskantar kalubalolin ta'addanci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China