in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU na fuskantar kalubale da dama a yayin da take kokarin yin gyaran fuska
2017-07-06 15:09:30 cri

A tsakanin ranakun 3 da 4 ga wata ne, aka shirya taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar tarayyar Afirka (AU) a hedkwatarta dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Taron na yini biyu, shi ne na farko da AU ta shirya, tun bayan zaben sabbin jami'an hukumar zartaswar kungiyar a watan Janairun bana.

Yanzu kasashen Afirka suna kokarin tinkarar kalubale daban-daban da ayyukan ta'addanci da bala'u daga indallahi, da matsalar rashin aikin yi da matasa ke fuskanta da kuma tangardar kasuwannin kasa da kasa, baya ga wasu manyan matsalolin da kungiyar AU ke fuskanta. Sakamakon haka, a yayin da sabuwar hukumar zartaswar kungiyar take kokarin yiwa kungiyar gyaran fuska, tana kuma fuskantar matsaloli iri iri.

Yawancin kasashen Afirka, ba su da cikakken tsarin masana'antu, galibinsu na dogara kan albarkatun halittu ne kawai wajen neman ci gaban tattalin arziki. Sakamakon haka, tattalin arzikinsu ya kan gamu da matsaloli idan kasuwannin kasa da kasa suka gamu da wata tangarda. A shekarun baya, sakamakon raguwar farashin muhimman kayayyaki a kasuwannin kasa da kasa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Afirka ya ragu sosai. Alal misali, tun daga shekarar bara kasashen Afirka ta kudu da Najeriya da yawan GDP nasu ya kai kusan rabin dukkan kasashen Afirka sun fuskanci koma baya, ba sa iya bayar da gudummawa kamar yadda ya kamata ga nahiyar Afirka, har ma lamarin ya yi tasirin kan tattalin arzikin Afirka a duk fadin duniya.

Sannan, ko da yake kasashen Afirka suna da dimbin matasa, amma ba su iya taka rawa kamar yadda ya kamata saboda galibinsu ba su iya samun aikin yi, har ma wasu daga cikinsu sun kama hanyar cin rani ba bisa doka ba.

A waje daya, game da batun tsaron kai, wasu kasashen Afirka na fuskantar barzanar hare-haren ta'addanci. Malam Moussa Faki Mahamat, sabon shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU ya nuna cewa, har yanzu kasashen Libya da Mali da Afirka ta tsakiya da Burundi da Kongo Kinshasha da kuma Somaliya suna cikin halin rashin kwanciyar hankali mai tsanani.

Bugu da kari, bala'u daga indallahi na kawo illoli ga aikin gona na kasashen Afirka sakamakon sauyin yanayin duniya. Bisa alkaluman da kungiyar kula da kaurar jama'a ta kasa da kasa ta bayar a watan Yunin da ya gabata ya nuna cewa, yanzu haka kimanin mutane miliyan 16 a yankunan gabashin Afirka suna cikin mawuyacin hali sakamakon bala'in fari, baya ga matsalar 'yan gudun hijira da ta kara tsanani.

A yayin taron kolin kungiyar AU na wannan karo, malam Moussa Faki Mahamat ya sanar wa shugabannin kasashen Afirka muhimman ayyukan da ya yi tun bayan da ya hau kan wannan mukami a watan Maris, inda ya umarci ofisoshin hukumar da su sake nazarin ayyukan da za a yi kamar yadda aka tsara da kuma tattauna muhimman ayyukan da za a yi a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Wani aiki mafi muhimmanci da Moussa Faki Mahamat ya ce zai yi shi ne yiwa kungiyar AU gyaran fuska. Ya ce, ya riga ya yi musayar ra'ayoyi da shugaba Alpha Conde na kasar Guinea, wato shugaban kungiyar AU na yanzu da shugaban kasar Rwanda wanda ke jagorantar aikin yiwa kungiyar ta AU gyaran fuska da shugaban kasar Chadi.

Wani aiki mafi muhimmanci da za a yi a lokacin da ake kokarin yiwa kungiyar AU gyaran fuska, shi ne fito da hanyoyin samun kudaden tafiyar da harkokin kungiyar daga kasashe mambobinta. Kungiyar AU ta dade tana dogaro kan tallafin kudin da kasashen duniya ke samar mata. Yawan kasafin kudin dukkan hukumomin kungiyar AU na shekarar 2017 ya kai dalar Amurka wajen miliyan 782, amma yawan tallafin kudin da aka samu daga waje ya kai kashi 74 cikin kashi dari. Sabo da haka, a yayin taron kolin kungiyar na shekarar 2016 da aka shirya a birnin Kigali, kungiyar AU ta tsai da kudurin cewa, tun daga shekarar 2017, dole ne dukkan kasashe mambobin kungiyar su bayar da kaso 0.2 cikin kashi dari, na harajin kudaden da ake karba daga kayayyakin dake shiga kasashen nasu ga kungiyar AU. Sakamakon haka, za a iya cimma burin tafiyar da ayyukan yau da kullum na kungiyar AU bisa kudin da kasashe mambobinta ke samarwa.

Malam Moussa Faki Mahamat ya sha yin kira ga kasashen Afirka da babbar murya da su hanzarta aiwatar da kudurin kungiyar AU kamar yadda ake fata. Amma ko da yake ya zuwa yanzu, kasashen Afirka 10 ne kawai wato Kenya da Rwanda da Habasha suka fara aiwatar da wannan kuduri, amma wasu kasashen Afirka suna ganin cewa, za su gamu da wasu matsaloli a lokacin da suke aiwatar da kudurin. Sabo da haka, malam Moussa Faki Mahamat ya ce, kungiyar AU za ta kafa wani kwamitin musamman mai kunshe da ministocin kasashen Afirka 10 domin tattauna batun gyara dabarar samun kudi da kungiyar take bukata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China