Mambobin kwamitin sun dauki wannan mataki ne yayin taronsu na 41 da ya gudana tsakanin ranakun 2 zuwa 12 ga watan Yulin wannan shekara.
Filin shakatawa na Comoe wanda aka kafa a shekarar 1968, yana daga cikin manyan wuraren shakatawa da suka yi suna a fannin nau'o'in tsire-tsire da dama a yammacin Afirka. Ko da yake filin ya fuskanci wasu matsaloli sakamakon na farauta, da gobara, da yadda wasu ke noma a cikinsa.
UNECSO ta ce yanzu haka wasu dabbobi kamar giwaye da gwaggwan birrai na kokarin bacewa a wurin, don haka ta ce tana shirin sanar da kasashen duniya barazanar da irin wadannan wuraren tarihi ke fuskanta don daukar matakan kare su. (Ibrahim)