in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Iraki sun yi nasarar kwato wasu yankuna daga hannun IS
2017-07-04 10:05:04 cri

Rundunar sojojin Iraki ta bayyana cewa, dakarunta sun yi nasarar kwato wasu sabbin yankuna da suka rage a hannun mayakan IS a tsohon birinn Mosul, bayan wata musayar wuta da ta haddasa mutuwar mayakan na IS da dama.

Wata sanarwa da rundunar hadin gwiwar sojojin Iraki ta fitar, ta ce runduna ta 16 ta sojojin Iraki sun kwato yankunan Khatoniyah, da Tuwalib da Ras al-Kour, biyo bayan halaka mayakan na IS kimanin 67 a filin daga

Sanarwar ta kuma ce, sojoji da suka kware a kwance abubuwan fashewa, sun yi nasarar kwance bama-baman da mayakan na IS suka dasa a filin daga, da nufin kawo cikas ga nasara da sojojin na Iraki ke samu.

Sashen yaki da ayyukan ta'addanci, da sojoji gami da 'yan sandan kasar Iraki, da ma dakarun kai agajin gaggauwa, sun dauki tsawon lokaci suna gumurzu da mayakan na IS a tsohon garin na Mosul, amma kuma dakarun suna samun nasara sannu a hankali sakamakon turjiyar da mayakan na IS ke nuna wa.

Tun a shekarar 2014 ne birnin na Mosul, da ma wasu yankunan arewaci da yammacin kasar Irakin ya fada hannun mayakan na IS.(Ibarhim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China