in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan raya yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka duk da kalubalen da ake fuskanta
2017-07-03 11:05:40 cri

A yayin jerin tarurrukan taron kolin kungiyar AU karo na 29 da yanzu haka ake gudanarwa a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, raya yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka yana da cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a wannan taro.

Sakamakon yawan kasashe a nahiyar Afirka, da kuma bambanci sosai wajen samun bunkasuwa a tsakaninsu, wannan ya sa kullum ake fuskantar matsala wajen inganta shawarwari game da yadda za a raya yankin cinikayya cikin 'yanci. Mahalarta taron kolin kungiyar AU na wannan karo suna ganin cewa, ana fatan samun nasara wajen raya yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka duk da tarin kalubalen da za a fuskanta a nan gaba.

Manufar kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka ita ce rage kudin harajin kwastan, kawar da shingen ciniki, da inganta cinikayya da zuba jari a tsakanin kasashen nahiyar, da kuma tabbatar da samun saukin zirga-zirgar jama'a da kayayyaki da kuma zuba jari a shiyyar, hakan taimaka wajen mai da kasashen nahiyar a matsayin wata babbar kasuwar bai daya. Tun daga watan Yuni na shekarar 2015 ne kasashe mambobin AU suka soma shawarwarin kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar, kuma ana sa ran za a cimma wadannan shawarwarin a watan Disamban shekarar 2017.

Mamban kungiyar AU mai kula da harkokin cinikayya da masana'antu Albert Muchanga ya bayyana a yayin taron kolin cewa, ana gudanar da shawarwarin kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar yadda ya kamata, kuma ana sa ran za a cimma yarjejeniya game da haka kafin karshen shekarar bana.

A nasa bangaren kuma, shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Moussa Faki ya bayyana cewa, dole ne a gaggauta raya yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka, hakan zai taimaka wajen ciyar da babbar nahiyar Afirka gaba. A yanzu haka kuma, kungiyar AU na duba yiwuwar kafa wata kungiyar kwarraru, don kula da ayyukan tsara yadda za a kafa yankin cinikin.

A shekarun nan, sakamakon raguwar farashin kayayyakin cinikayya masu yawa, da sake bullar matakan kariyar ciniki a duniya, kasashe da yawa na Afirka sun fuskanci raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu, wannan ya sa suka shiga cikin wani mummunan yanayin cinikayya. Bisa halin da ake ciki, kungiyar AU ta soma neman hanyar inganta tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

Sakataren zartaswa na hukumar kula da harkokin tattalin arzikin Afirka na MDD ya bayyana cewa, a sakamakon tasirin da rashin tabbas kan sakamakon tattalin arzikin duniya zai haifar a nan gaba, da rashin bunkasuwar zuba jari da dai sauransu, a shekarar 2017 mai yiwuwa saurin ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka zai ragu zuwa kashi 3.2 cikin dari, wato zai yi kasa sosai da matsakaicinsa ci gabansa a shekaru 10 da suka gabata wato kashi 5.4 cikin dari. Bisa wannan yanayin da ake ciki, tilas ne a zurfafa cudanya tsakanin kasashen Afirka a fannonin cinikayya da zuba jari, kuma wannan yana da muhimmanci kwarai wajen kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka.

Mamban kungiyar AU mai kula da harkokin cinikayya da masana'antu Albert Muchanga yana ganin cewa, kafa yankin cinikayya na da ma'ana kwarai ga tattalin arziki da al'ummar kasashen Afirka. Ya ce, sabbin alkaluman kididdiga na nuna cewa, yawan kudin cinikayya a tsakanin kasashen Afirka ya kai kashi 14 cikin dari kawai bisa na jimilar kudaden duk nahiyar. Kafa yankin cinikayya cikin 'yanci a nahiyar zai karfafa matsayin cinikayya a tsakanin kasashen Afirka, an kuma yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2021, wadannan kudade za su ninka har sau biyu."

Ko da yake ana samun ingantuwar kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka, amma halin musamman na kasashen nahiyar shi ke haifar da wasu kalubaloli ga wannan shiri

Rahotonni daga wajen taron kolin, na nuna cewa, kasashen nahiyar Afirka na fama da banbance-banbance a tsakaninsu ta fuskokin gudanar da harkokin kwastan da ma'aunin fasahohi, kuma wannan yana kawo matsaloli wajen neman dunkulewar kasuwar bai daya ta nahiyar. Baya ga haka, akwai bambanci a fannin matsayin bude kofa ga kasashen waje a tsakanin kasashen nahiyar, bambanci a fannin yadda kasashen ke rungumar yankin cinikayya cikin 'yanci. Ban da wannan kuma, wasu kasashe mambobin kungiyoyin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar ne, amma wasu ba su taba shiga irin wannan kungiya ba. Wadannan banbance-banbance da aka ambata a sama duk za su iya kawo cikas wajen fadada yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China