in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yankin Gulf sun baiwa Qatar wa'adin sa'o'i 48 da aiwatar da bukatun da suka nema
2017-07-03 09:47:18 cri

Rahotanni daga jami'an kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA na nuni da cewa, kasashen Larabawa 4 da suke zargin Qatar da goyon bayan ayyukan ta'addanci sun amince da bukatar da kasar Kuwaiti mai shiga tsakani ta nema ta tsawaita wa'adin da suka baiwa kasar Qatar cewa, ta hanzarta mayar da martani game da jerin bukatun da suka nema.

A ranar Lahadi ne dai wa'adin da kasashen 4 suka debawa Qatar din ke cika, kasashen dai sun hada da Saudi Arabia, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Masar, inda suka yanke shawarar tsawaita wa'adin ga Doha da ta hanzartar mayar da martani mai kyau bayan bukatar da Kuwaiti din ta nema, wacce ta kasance mai shiga tsakani domin warware takaddamar da ta kunno kai a tsakanin kasashen na yankin Gulf.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China