in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da IOC za su hada gwiwa game da shirya gasar Olympics ta lokacin hunturu a 2022
2017-07-03 09:28:03 cri

Kasar Sin da kwamitin shirya wasannin Olympic ta kasa da kasa (IOC) sun bayyana aniyarsu ta yin hadin gwiwa domin shirya gasar wasannin Olympic na lokacin hunturu a shekarar 2022.

A lokacin ganawa da shugaban kwamitin na IOC Thomas Bach a ranar Lahadi, mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, ya ambato batun ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai a helkwatar hukumar ta IOC a watan Janairun wannan shekara, ya ce wannan ziyarar mai dunbun tarihi ta nuna yadda dangantaka tsakanin kasar Sin da IOC ta kai wani sabon matsayi.

Yang ya ce, kasar Sin tana kokarin ci gaba da karfafa dangantaka da IOC domin samun gagarumar nasara wajen tabbatar da shirya gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu a shekarar 2022.

Bach ya yabawa kalaman mista Yang, kana ya yabawa irin gudumowar da kasar Sin ke baiwa wasannin na Olympic

Babban jami'in na IOC ya ce, ya yi amanna cewar, Sin za ta samun nasarar karbar bakuncin gasar wasannin na lokacin hunturu na shekarar 2022 bisa la'akari da irin hadin gwiwar dake tsakanin kasar ta Sin da IOC.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China