Sanarwar ta ce, kwamitin sulhun MDD ya nuna yabo ga babban ci gaban da kasar ta Cote D'ivoire ta samu, musamman ta fuskokin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da habaka tattalin arzikin kasar. Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta kammala aikinta a ranar 30 ga watan Yuni, wadda ta bayar da gudummawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman ci gaba a kasar ta Cote D'ivoire.
Har wa yau, sanarwar ta ce, bayan da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta kammala aiki, ya kamata Cote D'ivoire ta ci gaba da kokari a fannoni daban-daban, ciki har da yanke hukunci ga wadanda suka aikata laifi, da neman samun sulhu tsakanin al'ummomin kasar, da yin garambawul ga hukumomin tsaro, da kuma kara baiwa mata ikon shiga fagen siyasa.(Murtala Zhang)