in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Nijeriya ya fidda sharhi game da karfafa hadin gwiwar Sin da Nijeriya kan aikin rage talauci
2017-06-30 13:19:24 cri

Jiya Alhamis, jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya fidda wani sharhi mai taken "Alkawarin kasar Sin zuwa 2020: makomar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da tarayyar Nijeriya" a jaridar Daily Trust ta Najeriya. Dangane da wannan sharhi, ga karin bayani da abokin aikinmu Saminu Alhassan ya kawo mana:

A yayin dake halartar taron shawarwari kan rage talauci tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda aka yi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana ganin cewa, karni na 21 da ake ciki yanzu, ba na nahiyar Asiya ba ne kadai, har ma da nahiyar Afirka, da kuma kasashe masu tasowa. Ya ce, kamata kasar Sin da kasashen Afirka su dauki nauyin dake wuyansu cikin hadin gwiwa, domin kawar da talauci da kuma neman ci gaba. Kuma, wannan shi ne babban burin al'ummomin kasashen Sin da Afirka baki daya, da kuma bukatun bil Adama na neman ci gaba.

Haka kuma, a yayin taron, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat ya jaddada cewa, kasar Sin da kasashen Afirka sun tsai da kudurin kawar da talauci baki daya, kuma bayanai da fasahohin kasar Sin kan kawar da talauci na iya zama abin koyi ga kasashen Afirka.

Cikin littafi mai taken "kawar da talauci", an gabatar da ra'ayoyi da fasahohin shugaban kasar Sin Xi Jinping a fannin rage talauci da neman bunkasuwar yankin Ningde dake lardin Fujian na kasar, a lokacin da ya yi aiki a yankin a baya. Littafin ya kuma samu karbuwa sosai a yayin da aka gudanar da taron shawarwari game da rage talauci tsakanin Sin da kasashen Afirka wanda aka yi a birnin Addis Ababa.

Bugu da kari, fasahohi da ra'ayoyin da aka gabatar a cikin wannan littafi sun hada da: farawa daga ba da ilmi ga al'umma, da kuma mai da ci gaban tattalin arziki a matsayin burin siyasa mafi muhimmanci da dai sauransu, baya ga muhimman fasahohin kasar Sin wajen kawar da talauci, da neman ci gaba a birnin Ningde, a daya hannun na kunshe da kyawawan fasahohin da kasar Sin ta samu bisa matakanta na bude kofa ga waje.

Wadannan duka na da muhimmiyar ma'ana ga kasar Sin wajen cimma burinta na rage adadin yankuna masu fama da talauci a kasar, da kuma gudanar da ayyukan da suka shafi hakan.

Cikin shekaru 40 da suka gabata, mutane kimanin miliyan dari 7 na kasar Sin sun cimma nasarar kawar da talaucin dake addabar su, lamarin da ya ba da gudummawa kwarai da gaske ga MDD, wajen cimma burinta da ya kai kashi 70 bisa dari a shirin rage talauci ya zuwa shekarar 2015, lamarin da ya zama wata kyakkyawar nasara cikin kasashen duniya.

A shekarar 1949, watau lokacin da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin bai kai dallar Amurka biliyan 20 ba, ma'ana abun da ke hannun ko wane mutum guda bai kai dallar Amurka 35 ba, lamarin da ya sa a lokacin, kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashe mafiya fama da talauci a duniya.

Ya zuwa shekarar 1978, bayan kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bude kofa ga waje, ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasar ya kai biliyan 216.8, watau adadin abun da ke hannun ko wane mutum a kasar ta Sin ya kai dallar Amurka 277.

Haka zalika, ya zuwa shekarar 2016, ma'aunin GDP na kasar Sin ya riga ya wuce dallar Amurka biliyan dubu 10, adadin da ya wuce dallar Amurka dubu 8 a hannun ko wane mutum dake kasar. Lamarin da ya nuna cewa, bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kasar Sin ta samu wata hanyar da ta dace da halin da take ciki game da rage talauci, ta kuma yi amfani da halinta na musamman yadda ya kamata, wajen gudanar da ayyukan da suka shafi hakan, kamar batun yawan al'ummominta da ya kai biliyan 1.3, da kuma yin hadin gwiwa bisa manufar bude kofa ga waje. Lamarin da ya sa kasar ta kammala wani mawuyacin aikin da ba za ta iya kammala shi ba.

Kuma, bisa kididdigar da ake da ita a Nijeriya, an ce ya zuwa yanzu, akwai mutane kimanin miliyan 112 dake fama da talauci a kasar. A sa'i daya kuma, ya dace kasar Sin ta ba da taimako ga jama'arta sama da su miliyan 40, wajen kawar da talaucin su, domin cimma alkawarinta na kawar da talauci zuwa shekarar 2020. Lamarin da ya bude wani sabon shafi ga ci gaban hadin gwiwar tsakanin kasashen biyu, bisa manyan tsare-tsare.

Kasar Sin tana sa ran karfafa shawarwarin dake tsakaninta da tarayyar Nijeriya kan ayyuka a dukkan fannoni, yayin da take karfafa hadin gwiwar gwamnatocin kasashen biyu, domin neman wata hanya da za ta dace da Nijeriyar a fannin rage talauci tsakanin 'yan kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China