in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta ba masu kin biyan haraji wa'adin yafiya domin su gabatar da bayanan harajinsu na asali
2017-06-30 10:17:14 cri

Mukaddashin shugaban kasar Nijeriya Yemi Osinbajo, ya ba masu kin biyan haraji wa'adin yafiya na watanni 9, domin su daidaita matsayinsu na haraji ko a gurfanar da su gaban kuliya.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a Abuja, babban birnin kasar, yayin kaddamar da shirin bayyana kadarori da kudin shiga bisa radin kai, inda ya ce, idan suka gabatar da ainihin bayanansu, masu kin biyan haraji za su samu kariya daga gurfana gaban kuliya, sannan za a yafe musu laifin da kuma kudin ruwa dake taruwa kan harajin da ba a biya ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China