in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya yaba da kammalar aikin tawagar UNOCI
2017-06-30 09:53:28 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana farin ciki game da kammalar aikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalissar dake Cote d'Ivoire ko UNOCI a takaice.

Cikin wata sanarwa da kakakin sa Stephane Dujarric ya fitar, Mr. Guterres ya taya gwamnatin kasar Cote d'Ivoire murnar samun nasarar kawo karshen rikicin da ya haifar da kafa rundunar ta UNOCI.

Kaza lika babban magatakardar MDDr ya jinjinawa kwazon dukkanin sassan kasashe masu ruwa da tsaki a ayyukan rundunar, da masu ba da tallafi na shiyya shiyya da na kasa da kasa, wadanda suka taimaka wajen cimma nasarar ayyukan ta.

A ranar 30 ga watan nan na Yuni ne dai wa'adin aikin rundunar ta UNOCI ke cika a hukunci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China