in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron dandalin tattaunawar Davos ta yanayin zafi karo na 11
2017-06-29 18:40:55 cri
A yau Alhamis ne, aka rufe taron shekara-shekara na Davos na yanayin zafi karo na 11 a birnin Dalian dake bakin teku na kasar Sin. Taron na kwanaki uku ya jawo hallara wakilai sama da 200 daga kasashe da shiyyoyi fiye da 90, inda suka tattauna sosai kan kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, amfani da sabbin fasahohi da kuma sauran batutuwa.

Kwararrun da suka halarci taron, ciki har da shugaban WEF Klaus Schwab, shehu malamin jami'ar Harvard suna ganin cewa, yanzu haka tattalin arzikin duniya na farfadowa, amma duk da haka ana fuskantar hadari da kalubale a fannoni da dama. Haka kuma suna cike da imani kan karfin kasar Sin da matakan da kasar ke bi na neman ci gaban tattalin arzikin duniya. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China