"From Hong Kong to Beijing" wanda ke nufin "Daga Hong Kong zuwa Beijing" da Hausa, wani shirin Bidiyo ne na China Plus da ya kunshi babuka 5, wanda kowanne ke bada labarin wani mutum da ya fito daga yankin Hong Kong amma yake zaune a Beijing, babban birnin kasar Sin. Labarin ya kunshi wata daliba dake kokarin cimma burinta na zama 'yar tauraruwar fina-finai, da wani masanin fasahar sadarwa dake kokarin kyautata rayuwarsa; da wani dan wasan kwaikwayo dake ilmantar da yara; da likita mai gashin kashi dake kula da manyan masu wasannin motsa jiki da kuma dan kasuwa. Dukkan wadannan labarai na nuni ne da irin dangantaka ta kut da kut dake tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Hong Kong na kasar cikin shekaru 20 da suka gabata.