in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun harbi babban jami'in hukumar yaki da rashawa a Najeriya
2017-06-29 09:02:26 cri

Hukumomi a Najeriya sun fara gudanar da bincike don gano wadanda suka harbi babban jami'in hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC, wanda 'yan bingida suka harbe shi a birnin Fatakwal mai arzikin mai.

Austin Okwor, ya kasance babban jami'i a hukumar ta EFCC, ya samu raunuka a sakamakon harbin bindigar lokacin da maharan suka bude masa wuta a ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Shi dai jami'in ya kasance mutumin da ya jagoranci wasu muhimman ayyukan bincike da hukumar ta EFCC ta gudanar a kasar dake yammacin Afrika, ciki har da wasu zarge zargen aikata rashawa da ake yiwa wasu jami'an hukumar shari'a.

Dama dai gabanin kaddamar da harin a makon jiya, mista Okwor ya samu sakonnin gargadi, wanda ake zargin wadanda yake bincike kan su ne suka aika masa, kamar yadda hukumar EFCCn ta tabbatar da hakan.

Hukumar ta ce, tuni jami'an 'yan sanda suka fara gudanar da bincike, ciki har da batun sakonnin gargadin da aka aikewa jami'in.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China