Wani jami'in ofishin kididdigar kudade ta kasar (NAO) ne ya bayyana hakan,yana mai cewa, irin wadannan matakai sun hada da tsarin kason kudaden tsakanin kananan hukumomin, da yadda ake aiwatar da kasasfin kudi, magance matsalar kudi, da inganta matakan sanya ido.
Bayanai na nuna cewa, a 'yan shekarun nan, mahukunatan kasar Sin sun dauki kwararan matakai na magance fadawa hadarin basussuka. Baya ga yadda gwamnatin ta karfafa matakan bunkasa tattalin arzikin kasar. (Ibrahim)