in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya jaddada muhimmancin samar da guraben aiki
2017-06-28 13:17:44 cri

A jiya Talata, an bude taron shekara-shekara na New Champions, wato taron manyan kamfanonin kasa da kasa, karkashin laimar dandalin tattalin arziki na Davos, a birnin Dalian na kasar Sin.

Yayin taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi jawabi dangane da dabarun da kasar Sin ke bi don raya tattalin arzikinta.

Tun daga shekarar 2013, firaminista Li Keqiang na halartar tarukan shekara-shekara na manyan kamfanonin kasa da kasa 5 a jere, inda ya kan yi jawabi na musamman. A jawabinsa na wannan karo, Li ya bayyana muhimmancin ciyar da tattalin arzikin gaba, tare da more bangarori daban daban, da yadda kasar Sin take aiwatar da wannan manufa, bisa yanayin da ake ciki na samun dan ci gaban tattalin arziki, ko da yake hakan bai wadatar ba a sassan duniya.

A cewar firaministan kasar Sin, yadda ake daidaita tsarin masana'antu, bisa amfani da yanar gizo ko Internet, da fasahohin zamani na sadarwa, ya samar da sabbin kayayyaki tare da kara bukatun da ake da su. Wannan yanayi ya sa an samu karin damammakin tabbatar da samun ci gaba, tare da morewa bangarori daban daban. A cewarsa,

"Yanzu haka, mamoma Sinawa da suke zama cikin karkara sun samu damar sayar da amfanin gona zuwa manyan birane cikin sauri, ta hanyar fasahar sayar da kayayyaki ta yanar gizo. Hakan ya nuna cewa, idan mun samar da damammaki ga mutane, kuma suna da niyyar yin aiki, to, za su samu moriya sosai bisa damammakin."

Li Keqiang ya kara da cewa, har kullum kasar Sin tana kokarin aiwatar da manufar samun ci gaba tare da samun amfani ga bangarori daban daban. A shekarun baya, biranen kasar sun samar da guraben aikin yi har miliyan 13 a kowace shekara, yayin da marasa aikin yi suka kai kashi 5% kacal a cikin daukacin al'ummar kasar. A cewar jami'in,

"Mun dora muhimmanci sosai kan samar da guraben aikin yi, domin hakan shi ne tushe na samun ci gaba mai amfani ga kowa. A kasar Sin muna da ma'aikata fiye da miliyan 900, kuma a kowace shekara ana samun daliban da suka gama karatu, wadanda ke bukatar aikin yi kimanin miliyan 13, yayin da monama da yawa suke son yin kaura zuwa cikin birane. Wannan yanayi ya tilasta mana dora cikakken muhimmanci ga samar da isassun guraben aikin yi. Kuma dalilin da ya sa muke bukatar samun ci gaban tattalin arziki mai karko, shi ne domin samar da isassun guraben ayyukan yi da ake bukata."

Dangane da dabarun da ake amfani da su wajen samar da guraben aikin yi, Li Keqiang ya ce, kasar Sin tana sa kaimi ga daukacin al'ummarta, don su shiga aikin kafa sabbin kamfanoni, gami da kirkiro sabbin fasahohi. Kuma matakin da kasar ta dauka ya yi nasara, fiye da yadda aka zata a baya. Li ya ce,

"Tun da muka gabatar da mataki na karfafawa jama'a gwiwa domin su bude kamfanoni, da kuma kirkiro sabbin fasahohi a shekarar 2014, har zuwa yanzu muna samun karin kamfanoni dubu 40 a kowace rana, kuma kashi 70% daga cikinsu na gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Muna kokarin samar da dandali mai kyau ga masu niyyar bude kamfanoni domin rage kudin da za su kashe, da taimaka musu kafa kamfanoni cikin sauri."

Hakika yadda ake kokarin kafa kamfanoni da kirkiro sabbin fasahohi, ya riga ya zama wani yanayi na musamman na tattalin arzikin kasar Sin. Bisa alkaluman da aka gabatar dangane da kokarin kirkiro sabbin fasahohi a duniya a shekarar 2017, kasar Sin ta kasance ta 22 a duniya, wato matsayinta ya karu da maki 13, idan an kwatanta da shekarar 2013.

Ban da haka kuma, firaministan kasar Sin ya yi bayani kan yanayin da kasar Sin ke ciki a fannin tattalin arziki, inda ya ce tattalin arzikin kasar na ci gaba da karuwa, kuma tsarinsa na samun daidaituwa, saboda haka kasar za ta cimma burin da ta sanya gaba a fannin ciyar da tattalin arzikinta gaba, a shekarar 2017.

(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China