A yau kuma Talata 27 ga wata, aka bude taron na Davos na lokacin zafi, a babbar cibiyar taron kasa da kasa ta birnin Dalian, kuma za a kammala taron a ranar 29 ga wata.
Wakilai kimanin dubu 2 wadanda suka zo daga kasashe sama da 80, na halartar taron na wannan karo, wanda aka yiwa take da "bunkasuwar da aka samu bisa fahimtar juna, a yayin babbar kwaskwarimar masana'antu karo na hudu", inda za a yi tarurukan tattaunawa sama da 200, kan harkokin dake shafar yadda za a fuskanci kalubalolin dake duniya, da kyautata tsarin kasa da kasa da dai sauransu. (Maryam)