in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya game da farfado da yankin
2017-06-27 09:24:45 cri

Gwamnan jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya Muhammadu Bindow, ya jaddada kira ga gwamnonin yankin sa, da su kara kaimi wajen tabbatar da farfadowar yankin cikin gaggawa.

Gwamna Bindow, ya ce akwai bukatar kara azama wajen ganin an cimma nasarar kudurori 3, na sake raya yankin na arewa maso gabas, wadanda suka hada da sake tsugunar da al'ummu, da rage radadin damuwar al'ummu, tare da sake ginin yankin baki daya.

Ya ce, a yanzu haka, ayyukan da ake yi game da wannan manufa na tafiyar hawainiya, musamman a jihar Adamawa, inda sama da kaso 90 bisa dari na mazauna sansanonin 'yan gudun hijira suke komawa yankunan su na ainihi duk da kalubalen da suke fuskanta.

Bindow wanda ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin, ya ce masu gudun hijira 'yan jihar na ci gaba da fama da radadin halin da suka tsinci kan su ba tare da samun cikakken tallafin da ya dace ba.

A cewar gwamnan, kananan hukumomin Madagali, da Michika, da Maiha, da Mubi ta arewa, da Mubi ta kudu, da Gombi da Hong, na cikin yankuna da suka fi shan fama da matsalar rikicin kungiyar Boko Haram a jihar ta Adamawa. Ya ce, manyan kalubalen da jihar ke fuskanta a yankunan sun hada da lalacewar gajoji da hanyoyi, wanda hakan ke kawo tarnaki ga harkokin sufuri.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China