Yayin ganawar Li ya yaba da hadin kan dake tsakanin WEF da kasar Sin, ya kuma nuna cewa, Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen ketare don samar da yanayin da ya dace a fannin gudanar da harkokin cinikayya.
A nasa bangaren Klaus Schwab ya yaba sosai da manufofin da abun ya shafa da Sin ke gudanarwa, a cewarsa, WEF zai karfafa hadin kai tare da Sin, don taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya. (Bilkisu)