in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS na kitsa harin ta'addanci don daukar fansa sakamakon nasarar da aka samu kanta a Gabas ta Tsakiya
2017-06-26 13:25:25 cri

Masu nazarin al'amurra a Palestinu sun bayyana cewa, kungiyar IS tana kai hare hare ne a sassan duniya daban daban domin yin ramuwar gayya, sakamakon gagarumar nasara da ake samu na kakkabe ayyukan kungiyar a kasashen Syria da Iraki.

Mutane masu yawan gaske ne aka hallaka daga watan Maris zuwa yanzu inda galibi kungiyar IS din take daukar alhakin kaddamar da hare haren a kasashen Birtaniya, Faransa da Belgium, inda wadanda ake zargi da kaddamar da hare haren ta'addanci ke amfani da motoci, wukake, har ma da abubuwa masu fashewa, kuma suka kaddamar da hare haren kan jami'an 'yan sanda da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Ghassan Khatib, wani masani Bapalastinu ne, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yayin da IS take kara rasa iko da yankunan dake hannunta, wannan dalilin ne ya sa a halin yanzu take ta kokarin kaddamar da hare haren ta'addanci a matsayin mayar da martani.

Kwararren ya ce, matsalolin rikice rikice, da rashin samun ci gaba, gami da matsalar rashin aikin yi da komadar tattalin arziki a yankunan kasashen Larabawa, sun taimaka wajen kara bazuwar ayyukan IS a yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China