in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano gawawwakin mutane 10 da suka mutu a sakamakon bala'in gocewar kasa a garin Mao dake lardin Sichuan
2017-06-26 11:08:15 cri

Ya zuwa yanzu an gano gawawwakin mutane 10, baya ga wasu mutane 93 da suka bace a sakamakon bala'in zabtarewar kasa da ya auku a garin Mao dake lardin Sichuan na kasar Sin kwana biyu da suka gabata, inda kuma kawo yanzu ake ci gaba da kokarin aikin ceto.

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yong, ya jagoranci rukunin aiki na majalisar gudanarwar kasar da suka ziyarci garin na Mao don bada jagoranci ga aikin bada ceto, da sauran ayyuka samar da faruwar bala'in.

Kaza lika ofishin bada jagoranci ga bala'in a garin Mao ya bayar da labari a yammacin ranar 25 ga wata cewa, an riga an tsugunar da mutane fiye da 300 a wata makarantar firamare da otel dake garin dake dab da wurin. Har ila yau ofishin ya riga ya tura ma'aikatan musamman don taimakawa masu fama da bala'in don tausasa masu zuciya, tare da bayar da abinci da ruwa da sauran kayayyaki don tallafa masu.

An ce, sakamakon bala'in gocewar kasar na garin Mao, wasu kamfanonin kasar sun dauki matakai, tare da tura ma'aikata da kayayyaki zuwa wurin, tare da tabbatar da ganin an samar da wutar lantarki, da layukan sadarwa a wurin.  (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China