in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun bunkasuwa na Sin da kasashen Afirka ya zama babban dandalin kamfanonin Sin na zuba jari a Afirka
2017-06-26 10:58:36 cri

Yau Litinin 26 ga wata, rana ce ta cika shekaru 10 da kafa asusun bunkasuwa na Sin da kasashen Afirka, wato China-Africa Development Fund, ko CADF a takaice.

A kwanan baya, shugaban asusun na CADF mista Chi Jianxin, ya bayyana wa wakilinmu cewa, a matsayin asusun hada hadar kudi na farko dake mai da hankali kan zuba jari ga kasashen Afirka, asusun ya sa kaimi da nuna goyon baya ga kamfanonin Sin wajen zuba jari a kasashen Afirka, har ma ya riga ya zama wani muhimmin dandali a wannan fanni.

Daga watan Yuni na shekarar 2007, an fara gudanar da asusun CADF, wanda ya bayyana hakikanin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar Sin da kasashen Afirka. Bankin bunkasuwar kasar Sin ya ba da jagoranci kan wannan aiki. Kuma an tsara cewa, jimillar kudin asusun za ta kai dala biliyan 5 a karon farko. A watan Disambar shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shelanta a gun taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka cewa, za a kara kebe kudi dala biliyan 5 ga asusun CADF, wato jimillarsa ta kai dala biliyan 10 baki daya.

Bisa kokarin asusun CADF kuma, a cikin shekaru 10 da suka gabata, kamfanonin kasar Sin sun kara saurin shiga kasashen Afirka, wadanda suka sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a wurin, tare da kawo alheri ga jama'arsu. Shugaban asusun Chi Jianxin ya furta cewa, sabanin tsarin kudin agaji da rancen kudi, shi wannan asusun ya mai da hankali ne kan zuba jari ga nahiyar Afirka kawai, da zummar ba da taimako a fannin tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Ya ce,

"Asusun CADF yana kokarin gudanar da ayyuka masu karfin samar da dauwamammen ci gaba, da mayar da kudi ga kamfanoni. Jarin da aka zuba a wurin ba zai haddasa basusuka ba. A maimakon haka, jama'a za su ci gajiyarsu a fannin tattalin arziki da sauransu. Bugu da kari, kamfanonin za su ba da taimako a fannonin samar da guraben aikin yi, da buga haraji, da sha'anin kirkire-kirkire a kewaye da sauran wurare, haka ma a fannin tattalin arziki."

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, bayan kafuwar asusun CADF, an riga an yi shawarwari da kamfanoni sama da dubu daya, kan yadda za a yi hadin gwiwa da kasashen Afirka. Kuma ya bi sawu da yin nazari kan ayyuka sama da 500, da yanke shawarar zuba jari ga ayyuka 90 dake kasashen Afirka 36. Baki daya jimillarsu ta kai dala biliyan 4.3. Kamfanonin Sin sun kara zuba jari ga kasashen Afirka sama da dala biliyan 20 a fannonin manyan ayyukan more rayuwar jama'a, da samar da makamashi da aikin gona, da hakar ma'adinai da dai sauransu a sakamakon haka.

Kasar Masar, muhimmiyar kasa ce dake kan hanyar shawarar "Ziri daya da hanya daya". A shekarar 2013, asusun na CADF da kamfanin Fengshang na lardin Jiangsu sun kebe kudi tare, domin kafa kamfanin masana'antu na Masar na Fengshan a yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na Suez, a kokarin raya kasuwannin kasashen Afirka, da ba da tabbaci ga tsaron aikin gona, da rayuwar jama'a. shugaban kamfanin masana'antu na Masar na Fengshan, Li Xiangdong ya bayyana cewa,

"Hadin gwiwa tsakaninmu da asusun CADF ya shafi fannoni biyu, wato na'urar samar da harawa, da ajiye hatsi. A wasu yankuna, gwamnatocin kasashen Afirka sun mai da hankali sosai kan samun isasshen abinci. Shi ya sa bisa makomar nahiyar Afirka mai kyau, mun yi imanin cewa, za a sami ci gaba a wadannan fannoni biyu."

A Masar, asusun CADF ya zuba jari ga yankin hadin gwiwa kan tattalin arziki na Suez tsakanin Sin da Masar, da na'urar sanyaya daki ta Midea, da motar Huachen, da firijin Haier da sauransu. A duk nahiyar Afirka kuma, ya shiga ayyukan cibiyar samar da na'urorin gida ta kasar Afirka ta Kudu, da na kananan hanyoyin zirga zirgar jirgin sama na Ghana da sauransu.

Shugaban asusun Chi Jianxin ya bayyana cewa,

"An ba da shawarar 'Ziri daya da hanya daya' ga duk kasashen duniya. Hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka zai ci gajiyar hakan. Ba shakka, aiwatar da shawarar zai fadada kasuwannin kasashen Afirka a fannoni daban daban."(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China