in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane fiye da 200 sun mutu ko raunata a sakamakon gobarar da ta kama motar mai
2017-06-25 17:24:24 cri
Kafofin watsa labaru na kasar Pakistan sun bayar da labari cewa, mutane 140 sun mutu sannan fiye da mutane 100 sun samu rauni a sakamakon gobara a wata motar mai a yankin Bahawalpur na jihar Punjab dake gabashin kasar Pakistan. Yawan mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin zai iya karuwa domin wasu mutanen sun yi rauni mai tsanani.

Shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain da firaministan kasar Nawaz Sharif, sun nuna rashin jin dadi game da hadarin, kuma sun bukaci hukumomin da abin ya shafa da su ba da ceto cikin hanzari. Hafsan hafsoshin sojojin kasar Qamar Javed Bajwa ya bada umurni ga bangaren soja da su shiga aikin bada ceto, da tura jirgin sama mai saukar ungulu don bada gudummawa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China