in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dukkanin masu yawon shakatawa sun janye daga yankin da bala'in zabtarewar kasa ya afku a lardin Sichuan
2017-06-25 13:36:20 cri
Da misalin karfe 11 na daren jiya, cibiyar bada umurni ga ayyukan ceto dake garin Mao na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin ta kira taron manema labarai, inda mataimakin gwamnan yankin Aba na kabilun Zang da Qiang mai cin gashin kansa inda bala'in zabtarewar laka ya afku, ya bayyana cewa, yayin faruwar ibtila'in, akwai masu yawon shakatawa 142 wadanda suka yi bulaguro zuwa wurin. Yanzu an riga an tuntubi dukkaninsu, da kara sanin halin da suke ciki, kuma dukkansu sun rigaya suna janye daga wajen.

Bugu da kari kuma, an samu bayanai na mutane 118 wadanda suka bace, kuma za'a wallafa wadannan bayanai ba tare da bata lokaci ba a shafin Intanet na gwamnatin yankin Aba. Har wa yau kuma, gwamnatin yankin Aba ta bude wani layin waya na musamman, domin samun bayanai daga bangarori daban-daban game da mutanen da suka bace.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China