in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya nuna juyayi ga hasarar rayuka sakamakon zartarewar laka a kasar Sin
2017-06-25 13:14:50 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya nuna alhini sakamakon mummunan hasarar rayuka da aka samu a sanadiyyar zartarewar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin, inda mutane 120 zartarewar kasar ta binne su.

Hedkwatar aikin ceto ta kudu masu yammancin lardin ta sanar da cewa, da misalin karfe 10 na dare agogon yankin masu aikin ceto sun tono gawawwakin mutane 15.

Mista Gutteres ya jinjinawa tawagar jami'an bada agaji na kasar, kana ya ce MDD a shirye take ta ba da dukkan taimakon da hukumomin kasar Sin ke bukata.

An shafe dare guda ana cigaban da aikin ceton, inda dubban masu aikin ceto ke cigaba da gudanar da ayyukansu a yankin ta hanyar amfani da na'urorin hangen karkashin kasa da karnuka masu iya sansano abubuwan dake binne a karakshin kasa. Sai dai alamu na baya bayan nan na nuna cewa ba su gano alamun akwai abu mai sauran numfashi a karkashin kasa ba.

Babban sakataren ya aike da sakon ta'aziyya ga al'umma kasar da gwamnatin Sin bisa hasarar rayuka da aka samu, kana ya yi fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China