Daraktan shirin bada agajin gaggawa na Asusun Manuel Fontaine, ya bayyana a jiya cewa, barazanar barkewar cututtukan a kasashen Kamaru da Chadi da Niger da Najeriya, na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara fuskantar rashin tsaro da karin zirga-zirgar jama'a, musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da kuma ambaliyar ruwa da rashin kyawun titi, zai yi gagarumin tasiri wajen rage isar kayayyakin jin kai zuwa wurare masu nisa.
Manuel Fontaine ya kara da cewa, UNICEF da sauran hukumomin abokan huldarsa, na aiki a yankin na tafkin Chadi, a wuraren da ke fuskantar hadarin barkewar cutar amai da gudawa, inda suke ilmantar da iyalai illolin dake tattare da cutar da kuma matakan da za su iya bi na kare kawunansu.
Duk da rashin kudi, jami'in ya ce UNICEF a bana, ya kuduri niyyar samarwa mutane miliyan 2.7 da tsafatataccen ruwa da suke bukata don rayuwa. (Fa'iza Mustapha)