Gwamnatin Masar ta yanke shawarar tsawaita dokar ta baci da ta sanya a kasar da watanni uku.
Jaridar Ahram ta kasar ta ruwaito cewa, gwamnatin ta yanke shawarar ne yayin taron majalisar zartarwar kasar da ya gudana jiya.
A ranar 11 ga watan Afrilun da ya gabata ne, majalisar dokokin kasar ta amince da matakin fadar shugaban kasar na sanya dokar ta baci na watnni uku a kasar, biyo bayan hare-hare bam da aka kai kan wata mujami'a, da suka yi sanadin mutuwar mutane 44.
A nata bangaren, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta sanar a jiya Alhamis cewa, sojoji sun kashe mutane 7 dake da alaka da hare-haren dake nuna adawa da kiristoci.
Ma'aikatar ta kara da cewa, sai da 'yan ta'addan da suka buya a yankin Assuit mai tsaunuka, suka yi musayar wuta da sojojin kafin a kashe su.
Tun bayan hambarar da Mohammed Morsi a shekarar 2013 ne kasar Masar ke fama da hare-haren ta'addanci. (Fa'zia Mustapha)