in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Turai 6 sun tusa keyar 'yan Nijeriya 34 zuwa gida
2017-06-23 09:17:54 cri

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce, a kalla 'yan kasar 34 da aka tusa keyarsu daga wasu kasasehen Turai 6, bisa laifukan da suka danganci shige da fice, sun isa filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammed dake jihar Lagos ta kasar.

Kakakin ofishin 'yan sanda dake filin jirgin saman Joseph Alabi, ya ce an tusa keyar mutanen ne daga kasashen Switzerland da Jamus da Iceland da Austria da Belgium da kuma Hungary.

Mutanen sun hada da maza 32 da mata 2, kuma an dauko su ne cikin jirgin Airblue Panorama da aka yi shatarsa.

Joseph Alabi, ya ce ana zargin mutanen da aikata laifukan da suka danganci shige da fice a kasashen da suka je.

Ya kuma kara da cewa, hukumomin kula da shige da fice a Nijeriya sun dauki bayanan su, kafin daga bisani suka tafi garuruwansu.

Ko a watan Afrilu, sai da kasashen Turai 9 suka mai da 'yan Nijeriya 90 zuwa gida, bisa aikata irin wadancan laifuka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China