in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da shirin tantance ingancin manyan filayen jiragen sama na Najeriya
2017-06-23 09:11:00 cri

Kakakin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman ta Najeriya (NCAA) Sam Adurogboye ya ce, shirin nan na tantance ingancin filayen tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legos da takwaransa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja na tafiya kamar yadda aka tsara.

Da yake yiwa taron manema labarai karin haske game da shirin a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar, ya ce, hukumar ta NCAA tana aiki kafada da kafada da wakilan hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa(ICAO) mai kula da kasashen yammaci da tsakiyar Afirka (WACAF) don tabbatar da kammalar aikin cikin watan Yulin wannan shekara.

Hukumar ICAO mai kula da kasashen yammaci da tsakiyar Afirka wato WACAF a takaice ce take gudanar da wannan aiki, karkashin wani shiri na tabbatar da ingancin jiragen dake shawagi a yankin kasashen Afirka da tekun Indiya (AFI).

An amince da wannan shiri ne dai yayin babban taron hukumar ICAO na 36 da nufin tabbatar da tsaron jiragen sama dake zirga-zirga a yankin kasashen Afirka da tekun Indiya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China