in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na fatan kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya"
2017-06-22 20:24:41 cri

A yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin, ya bayyana a Beijing cewa, kasarsa na fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin ta fuskar ma'adinai, da makamashi, da aikin gona da dai sauransu, a kokarin kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya".

Mista Bawumia, ya fadi hakan ne yayin da yake halartar taron dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Ghana dangane da harkokin ciniki da zuba jari, wanda hukumar bunkasa harkokin ciniki ta kasar Sin, da ofishin jakadancin Ghana da ke kasar Sin suka yi hadin gwiwar shiryawa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China