Liu Jieyi ya bayyana cewa, Sin tana fatan kasashen duniya za su kara yin mu'amala da juna kan fasahohin magance kwararowar hamada, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a wannan fannin, da hada kai tare don samun ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba, da gina duniya mai tsabta da kyaun gani.
Wakilan kasashen Afirka ta Kudu, Iran, Tunisia da Senegal da sauransu dake MDD sun yaba ma kasar Sin kan kokarinta na inganta hadin gwiwar kasa da kasa a fannin magance kwararowar hamada. Sun kuma yi nuni da cewa, Sin ta taimakawa kasashe masu tasowa wajen inganta karfinsu na magance kwararowar hamada da raya matakan samar da hatsi, da kyautata yanayi da muhallin halittu. (Zainab)