in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin zuba jari a Afirka ta yadda nahiyar za ta samu ci gaba da kanta
2017-06-21 13:07:05 cri

A ranar 26 ga watan Yunin shekarar 2007 ne, aka kafa asusun raya Afirka na kasar Sin a hukunce, wannan shi ne asusun zuba jari a sassa masu zaman kansu na farko da Sin ta kafa game da kasashen Afirka, wanda kuma ya kasance wani muhimmin mataki na taron kolin Beijing game da dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka na shekarar 2006. A gabanin ranar cika shekaru 10 da kafa asusun, wakiliyar mu ta kai ziyara ta musamman ga shugaban asusun mista Chi Jianxin.

A yayin zantawarsu, mista Chi Jianxin ya yi farin ciki kwarai da kokarin asusun raya kasashen Afirka na kasar Sin ya yi a fannin jagoranci da goyon bayan kamfanonin Sin da su kara zuba jari a kasashen Afirka, hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasashen Afirka samun ci gaba bisa karfin kansu.

Mista Chi ya ce,

"Mun nuna goyon baya ga kamfannoni da masana'antun dake samar da na'urori na zamani na kasar Sin don su zuba jari a Afirka, ta yadda za a karfafa hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, tare kuma da inganta hadin kai a tsakannin kasashen Afirka da sauran kasashe masu ci gaba a wadannan fannoni. Baya ga haka, ta hanyar zuba jari da hadin kai, za a inganta bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasashen Afirka, da kara yawan kudaden haraji da aka samu, da yawan kudin da ake samu ta hanyar fitar da kayayyaki da dai sauransu, hakan ya kara karfin kasashen na neman dauwamammen ci gaban tattalin arziki da na al'umma."

Kamar yadda mista Chi ya bayyana a baya, a cikin shekaru 10 da suka gabata, asusun raya Afirka na kasar Sin ya goyi bayan kamfannonin kasar Sin da su hada kai tare da kasashen Afirka, kuma an samu sakamako mai kyau wajen inganta raya masana'antun kasashen Afirka ta hanyar zuba jari. Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, bayan kafuwar asusun, yawan jarin da Sin ta zuba ma Afirka kai tsaye ya karu daga dalar Amurka biliyan 2.56 a shekarar 2006, zuwa dala biliyan 34.7 a shekarar 2015. Ya zuwa yanzu, asusun ya zuba jarin sama da dalar Amurka biliyan 4.3 ga ayyuka 90 na kasashen Afirka 36, wadanda suka shafi samar da kayayyaki, muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, aikin gona da dai sauransu, ciki har da yankin masana'antun samar da kayayyakin lantarki da ake amfani da su a gida da aikin samar da siminti na kasar Afirka ta kudu, da aikin reshen hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama na AWA na Ghana, da kuma aikin tashar jiragen ruwa ta manyan sundukan daukan kayayyaki ta Legos ta Najeriya da dai sauransu.

Mista Chi ya nuna cewa, akwai bambanci a tsakanin samar da tallafi da samar da rancen kudi maras ruwa, jarin da asusunsa ke amfani da su a fannin raya kasashen Afirka kudin ne na kasuwanci, saboda haka, wannan ya taimakawa kasashen Afirka raya karfin kansu, da neman ci gaba bisa karfin kansu.

"Asusun raya Afirka na kasar Sin, asusun zuba jari ne, amma yana ba da tallafi ko rancen kudi ba tare da ruwa ba. Asusun na kokarin neman ayyukan dake samar da dauwamammen ci gaba da riba a fannin tattalin arziki. Irin wannan zuba jari ba zai kara nauyin dake kan kasashen Afirka ba, a maimakon haka zai amfanawa kasashen wajen kara samar da guraban aikin yi, da samun kudaden haraji, ta yadda za a samar da dauwamamman ci gaba ga tattalin arzikin kasashen."

A shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar hadin kan kasa da kasa ta "Ziri daya da hanya daya", nan da shekaru hudu da masu zuwa, abubuwan da shawarar ta shafa sun karu, wadanda suka shafi yankunan Asiya, Turai da kuma Afirka. Amma, wasu na yiwa ra'ayin kuskuren fahimta cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" za ta rage matsayin kasashen Afirka a fannin hadin kai a tsakanin Sin da kasashen ketare. Game da haka, mista Chi ya ce,

"Kofar Shawarar 'Ziri daya da hanya daya' a bude take ga dukkan kasashe, hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka zai kara bunkasa karkashin wannan shawara. 'Manyan ayyukan hadin kai guda goma tsakanin Sin da Afirka" da shugaba Xi ya gabatar, da 'Hadin kan Sin da Afirka kan samar da kayayyaki', da 'Hadin kan Sin da Afirka a fannin masana'antun kere-kere' da muke gudanarwa a yanzu, dukkansu suna dacewa da shawarar 'Ziri daya da hanya daya'. Shawarar za ta inganta fitar da wasu kayayyakin da kasashen Afirka suka samar zuwa kasashen da shawarar ta shafa, kuma ba shakka kasuwar kasashen Afirka za ta habaka sakamakon wannan shawara." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China