in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara shawarwari game da ficewar kasar Birtaniya daga EU
2017-06-20 13:47:21 cri

A jiya Litinin ne, aka fara shawarwari game da ficewar kasar Birtaniya daga EU a hukunce, a wani mataki na kawo karshen dangantakar dake tsakanin Birtaniya da EU ta tsawon shekaru fiye da 40. Babban jami'in EU mai kula da harkokin ficewar Birtaniya daga EU Michel Barnier ya bayyana a wannan rana cewa, akwai yiwuwar cimma yarjejeniya mai adalci a tsakanin EU da Birtaniya, hakan zai taimaka wajen cimma daidaito.

An fara shawarwari game da ficewar kasar Birtaniya daga EU a cibiyar EU dake Brussels, inda Babban jami'in EU mai kula da harkokin ficewar Birtaniyar daga EU Michel Barnier da jami'in kasar Birtaniya mai kula da hakokin ficewa daga EU David Davis suka yi shawarwarin. Wannan rana kusan cika shekara daya ke nan da aka kada kuri'un jin ra'ayoyin jama'a a kasar Birtaniya game da ficewar kasar daga EU, kana kusan watanni 3 da firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta mika wakisar janyewar kasarta daga EU ga kungiyar EU.

Barnier ya bayyana a cibiyar kungiyar EU cewa, da farko yana jajantawa jama'ar kasar Birtaniya sakamakon harin ta'addanci da ya faru a wannan rana. Ya jaddada cewa, burin shawarwarin shi ne daidaita matsalar rashin tabbas da jama'ar kasar Birtaniya za su shiga bayan da kasar ta janye daga EU. Ya bayyana cewa,

"Burinmu shi ne warware matsalar rashin tabbaci a sakamakon ficewar Birtaniya daga EU, musamman kula da jama'a, da wadanda za su amfana da manufofin EU, da kuma tasirin da hakan zai yi kasashen dake kan iyakokin kasar, musamman kasar Ireland. Ina fatan za a tabbatar da ayyukan da za a gudanar da farko da jadawalinsu, ta yadda zan gabatar da rahoto ga majaliasar Turai game da shawarwarin a wannan mako."

Bayan da aka yi shawarwarin a kwana na farko, Barnier ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana da yamma cewa, wannan taro mafari mai ma'ana ne. Ya bayyana cewa,  

"Yau, mun cimma daidaito kan jadawali da tsarin hukumomi da muhimman batutuwan da muke tattaunawa. A mataki na farko, tilas ne mu warware matsalar rashin tabbas a sakamakon janyewar Birtaniya daga EU. Muna son tabbatar da janyewar yadda ya kamata. A mataki na biyu, za mu tattauna yadda dangantakarmu za ta kasance a nan gaba."

Barnier ya jaddada cewa, cimma yarjejeniya a tsakanin bangarorin biyu shi ne mafi kyau maimakon rashin cimmawa. Ya bayyana cewa,

"Akwai yiwuwar kungiyar EU da kasar Birtaniya za su cimma wata yarjejeniya mai adalci, wannan yana da kyau sabanin gaza cimma daidaito. Wannan shi ne dalili da ya sa muke kokarin yin hadin gwiwa tare da kasar Birtaniya, ba nuna kiyayya gare ta ba."

A gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana, jami'in kasar Birtaniya mai kula da harkokin ficewar Birtaniya daga EU David Davis ya bayyana cewa, an cimma nasarori a shawarwarin, bangarorin biyu suna fatan cimma sakamako mai kyau. Ya bayyana cewa,

"Bayan da aka kada kuri'un jin ra'ayoyin jama'a a kasar Birtaniya, mun shaida cewa, burinmu na farko shi ne samar da tabbaci ga jama'ar kasashe membobin EU dake kasar Birtaniya da jama'ar kasar Birtaniya dake kasashe membobin EU. Don haka, muna da imanin tare da kammala wannan aiki bayan da aka fara shawarwarin don samar da tabbaci cikin hanzari."(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China