in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin tallafawa 'yan gudun hijira Falasdinawa
2017-06-19 13:50:40 cri

Ranar 20 ga watan da muke ciki ita ce "ranar 'yan gudun hijira ta duniya", wato ranar da MDD ta kebe domin jaddada bukatar ba da agaji ga 'yan gudun hijira. Bisa taken wannan rana, idan an yi nazari kan bayanan 'yan gudun hijira a kasashe daban daban, za a lura da cewa cikinsu akwai Falasdinawa kimanin miliyan 5. To, wadanne matakai gwamnatin kasar Sin ta dauka domin tallafawa Falasdinawan?

Yayin da Chen Xingzhong, darektan ofishin kasar Sin a Falasdinu, yake hira da wakilin CRI, ya ce an dade ana fuskantar matsalar 'yan gudun hijira a Falasdinu, ganin yadda a shekarar 1949, MDD ta kafa ofishin ba da agaji ga 'yan gudun hijira Falasdinawa, domin samar da taimako a fannonin ilimi da na jinya. A namu bangare ma, kasar Sin tana dora muhimmanci matuka ga lamarin, abin da ya sa take kokarin tallafawa 'yan gudun hijira Falasdinawa ta hanyoyi daban daban. Jami'in ya ce,

"Kasar Sin tana kokarin samar da agaji ta hanyoyi daban daban. A fannin hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin duniya, kasar Sin tana samar da kudi ga ofishin ba da agaji ga 'yan gudun hijira Falasdinawa na MDD a kowace shekara. Sa'an nan a watan Oktoban bara, yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Faransa, ya ambaci mawuyacin halin da 'yan gudun hijira Falasdinawa suke ciki. Ya ce a lokacin da ake mai da hankali kan yanayin da kasashen Syria da Libya ke ciki, bai kamata ba a manta da batun 'yan gudun hijira Falasdinawa, wanda ya kasance irinsa na farko da aka samu a gabas ta tsakiya. Saboda haka, kasar Sin na ta kokarin tallafawa 'yan gudun hijirar, da goyon bayan shawarwarin da za a yi tsakanin Falasdinu da Isra'ila, tare da fatan za a cimma nasara cikin hanzari."

Har ila yau, jami'in kasar Sin ya yi bayani kan matsayin da kasar Sin ke dauka dangane da maganar Fadasdinu, ya ce,

"Da farko, shugabannin kasar Sin sun gabatar da wasu shawarwari. Ga misali, a shekarar 2013, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da shugaba Mahmoud Abbas a birnin Beijing na kasar Sin, inda shugaba Xi ya gabatar da shawarwari 4 kan yadda za a daidaita batun Falasdinu. Daga bisani a shekarar 2016, yayin da shugaba Xi Jinping ke ziyara a kasar Masar, ya sake yin bayani kan matakan da za a iya dauka don daidaita maganar Falasdinu. Sa'an nan, a watan Mayun bana, yayin da ya yi jawabi a bikin bude dandalin hadin gwiwar kasashen duniya na 'ziri daya da hanya daya', shugaba Xi ya bayyana cewa, yankunan da hanyar siliki ta bi sun taba kasancewa ni'imtattun wurare masu wadata, sai dai zuwa yanzu, da yawa cikinsu sun zama wuraren da ake samun tashin hankali da tarzoma. A cewar shugaban kasar Sin, bai kamata ba a bari yanayin wuraren ya ci gaba da lalacewa. Maimakon haka, kamata ya yi a yi hadin gwiwa a fannin aikin tsaro, da kokarin daidaita matsalar ta hanyar shawarwari da sulhuntawa, da nacewa ga adalci da gaskiya."

Ban da haka kuma, Chen Xingzhong ya ce, abu na biyu da ya shaida yadda kasar Sin take dora muhimmanci sosai kan batun Falasdinu, shi ne kokarin da kasar ta yi don shiga tsakani da kuma neman sanya bangarori masu ruwa da tsaki su koma teburin shawarwari. A cewarsa,

"A shekarun baya, shugabannin kasar Sin sun ziyarci Falasdinawa da Isra'ila daya bayan daya, inda dukkansu suka yi kokarin lallashin bangarori masu ruwa da tsaki don su koma kan teburin shawarwari. Ga misali, tsohon firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da babban sakataren fadar shugabancin Falasdinu Tayeb Abdelrahim, dukkansu sun ziyarci kasar Sin a shekarar da muke ciki, inda shugabannin kasar Sin suka yi kokarin isar da sakon duniya na nema a daidaita matsalar dake tsakaninsu ta hanyar sulhu."

Haka zalika kasar Sin tana kokarin taka rawa a bukukuwan da aka kira a duniya don neman samun sulhu tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna a yankin gabas ta tsakiya. A cewar Chen Xingzhong, kullum kasar Sin tana nuna matsayin da ta dauka dangane da batun Falasdinu a fili domin kowa ya fahimta. Jami'in ya ce, kasar Sin tana goyon bayan yunkurin yin shawarwari tsakanin Falasdinu da Isra'ila, kuma tana goyon bayan shawarar kafa kasashe 2 masu zaman kansu. Ban da haka kuma kasar Sin tana nunawa Falasdinu goyon baya, domin ta yi amfani da gabashin birnin Kudus a matsayin fadar mulkinta, sa'an nan ta kafa wata kasa mai mulkin kanta.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China