A wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, bayan bacewar jami'an biyu, Pakistan ta yi mu'amala da Afghanistan nan take, inda ta bukaci Afghanistan din da ta ceto su, kuma ta tabbatar ta yi iyakacin kokarinta domin cafke wadanda suka aikata wannan danyen aiki. Sanarwar ta ce, Afghanistan ta riga ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan batun.
Tun da farko, kafofin yada labarai na Pakistan sun ba da labari cewa, wadannan jami'ai biyu sun yi aiki a karamin ofishin jakadancin Pakistan a birnin Jalalabad na Afghanistan. A ranar Jumma'a 16 ga wata, sun bace a kan hanyarsu ta komawa kasar Pakistan, ba su isa Torkham cikin lokaci ba.
Jakadan Afghanistan a Pakistan Omar Zakhilwal ya tabbatar da wannan batu.
Kawo yanzu babu wata kungiyar da ta shelanta daukar alhakin bacewar tasu.(Fatima)