in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta bukaci UNSC ya tsame dakarun dake tsaron fadar shugaban kasar daga haramcin makaman da aka kakabawa kasar
2017-06-19 10:00:47 cri

Mahukuntan kasar Libya sun yi kira ga kwamitin tsaron MDD da ya tsame dakarun dake tsaron fadar shugaban kasa daga haramcin shigo da makaman da kwamitin tsaron majalisar ya kakabawa kasar.

Babban kwamandan dakarun dake tsaron fadar shugaban kasar ta Libya Janar Najmi al-Nakou wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce, bai kamata wannan haramci ya shafi dakarun fadar shugaban kasar ba, ganin cewa a shekara da ta gabata ce aka kafa dakarun, kuma aikinsu shi ne kare kayayyakin gwamnati da kan iyakokin kasar da ba da kariya ga jami'an gwamnatin da kuma tawagar jami'ai da suka kawo ziyara kasar.

Janar al-Nakou ya kara da cewa, dakarun fadar shugaban kasar ba su da alaka da wata jam'iyyar siyasa, duba da cewa an kafa rundunar ce karkashin yarjejeniyar siyasar kasar da aka cimma da nufin tabbatar da doka da oda a cikin kasar.

Al-Nakou ya yaba da rawar da tawagar MDD dake Libya ke takawa gami da goyon bayan da shawarwarin tsaro da take baiwa dakarun tsaron fadar shugaban kasar.

A watan Mayun shekarar 2016 ne firaminisan kasar ta Libya da MDD ke marawa baya Fayez Sarraj, ya gabatar da wata shawara mai lamba 2, da nufin kafa rundunar tsaron fadar shugaban kasar mai kunshe da sojoji da 'yan sanda wadda za ta kasance a Tripoli, babban birnin kasar.

Sai dai kuma rundunar sojojin kasar karkashin jagorancin janar Kahilfa Haftar dake gabashin kasar, ba su goyin bayan kafa wannan runduna ba, saboda yunkurin da suka ce sun yi na kwace iko da rundunar sojojin kasar, zargin da al-Nakou ya karyata.(Ibarhim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China