in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yaba ma kasar Sin kan kokarin da take na kawar da talauci
2017-06-17 12:50:35 cri
Kungiyar sa kaimi ga mu'amalar da ake yi tsakanin jama'a da asunsun kawar da talauci na kasar Sin, sun kira wani taron gefe mai taken 'kiyaye hakkin dan Adam ta hanyar rage talauci' a jiya Juma'a, yayin da ake gudanar da taro karo na 35 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD a Geneva na kasar Switzerland.

Yayin taron, wani masanin ilimin dabarar kawar da talauci na kasar Sin Wang Xiaolin, ya ce, kasar Sin ta yi nasarar rage yawan jama'ar kasar masu fama da tsananin ta'auci da miliyan 800 cikin shekaru 30 da suka wuce, kuma wannan nasara da aka cimma a dukkan fannonin rage talauci da kare hakkin dan Adam, ta janyo hankalin al'ummomin kasa da kasa.

A na sa bangaren, babban darektan kungiyar Mercy Corps mai tallafawa matalauta a duniya, mista Henri van Eegen, ya ce kasar Sin tana kan gaba a duniya a fannin yaki da talauci, kuma ya kamata a yayata dabarun da kasar ta dauka a wannan fanni zuwa sauran kasashe.

Sai dai a cewarsa, duk da cewa kasar Sin da wasu kasashe sun bada gudunmowa sosai wajen kawar da talauci a duniya, har yanzu akwai mutane fiye da miliyan 100 da ke fama da talacui a duniya.

Don haka ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara hada gwiwa, sannan gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu da fararen hula su hada karfi ta yadda za a samu damar kawar da talauci daga doron kasa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China