in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cuba ta nuna rashin jin dadi kan yadda Trump ya tsaurara manufofi a kanta
2017-06-17 12:48:22 cri
Dangane da sabuwar manufar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar akan kasar Cuba, gwamnatin kasar ta fitar da wata sanarwa a jiya Jumma'a, tana mai bayyana matakin a matsayin mai da hannun agogon baya dangane da huldar dake tsakanin kasashen 2.

Baya ga haka, gwamnatin kasar Cuba ta jaddada cewa, duk wani yunkuri na neman matsa mata lamba don canza tsarin kasar ta fuskokin siyasa, tattalin arziki da zaman al'umma ba zai yi nasara ba.

A don haka, tsaurara manufofi da Amurka ta yi akan Cuba, ba zai yi tasiri kan kokarin kasar na neman ci gaba ba, haka kuma ba zai sanya jama'ar kasar su saduda ba, in ji gwamnatin kasar ta Cuba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China