Mummunar takarar da manyan kasashen duniya suke yi ba ta dace da moriyar kasashen duniya ba ciki har da kasar Sin
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau a nan birnin Beijing cewa, a ganin kasar Sin, mummunar takarar da manyan kasashen duniya suke yi ba ta dace da moriyar dukkan kasashen duniya ba ciki har da kasar Sin.
Lu Kang ya bayyana hakan yayin da aka yi tambaya game da kalaman da sakataren harkokin tsaron kasar Amurka James Mattis ya yi a kwanakin baya cewa, Rasha da Sin da sauran kasashe sun kara samun karfi a fannin aikin soja, wannan ya sa kasa da kasa suke fuskantar hadarin komawa yanayin yin takara a tsakanin manyan kasashen duniya. (Zainab)