in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan mahukuntan yankin Taiwan za su fahimci hakikanin yanayin da ake ciki
2017-06-14 15:12:59 cri
A jiya Talata 13 ga watan nan ne Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta rattaba hannu kan hadaddiyar sanarwar kulla huldar diplomasiyya tsakaninta da Jamhuriyar kasar Panama.

A yau Laraba kuma, kakakin ofishin kulawa da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Ma Xiaoguang ya yi sharhi kan wannan batu. A gun taron manema labaru yana mai cewa, batun ko dangantakar dake tsakanin babban yanki da yankin Taiwan na Sin za ta koma daidaitacciya, hakan na dogaro kan shawarar da mahukuntan yankin Taiwan za su yanke. Mr. Ma ya yi fatan za a samu fahimtar hakikanin yanayin da ake ciki, su kuma dora niyya wadda ta dace.

Game da batun kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Panama, Ma Xiaoguang ya bayyana cewa, kasar Sin daya ce tak a duk fadin duniya. Kuma kasa da kasa suna bin manufar kasar Sin daya tak, yayin da kowa ke amincewa da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasashen biyu. Kana wannan ba batu ne na musayar moriyar cinikayya ba ce.

Ban da haka, Ma ya kara da cewa, kowa ya sani, ana daidaita harkokin waje na yankin Taiwan bisa manufar kasar Sin daya tak. Kana ana fatan mahukuntan yankin Taiwan za su dora niyya da ta dace game da batun babban tushe a fannin siyasa na raya dangantaka tsakanin bangarorin biyu dake mashigin tekun Taiwan cikin lumana, ta yadda za a aza tubali mai kyau, na raya dangantaka tsakaninsu cikin dogon lokaci. (Fatima Liu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China