A ranar Litinin 12 ga wata ne shugaban Panama, Juan Carlos Valera ya yi jawabi ta telibijin, inda ya sanar da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Panama da Sin. Julio Chur ya taba zama mai ba da shawara kan harkokin diplomasiyya na tsohon shugaban kasar Martin Torrijos. Ya kuma taya murna ga gwamnatin Valera bisa niyyarta a daukar wannan mataki, ya kuma ce daukar wannan mataki ga gwamnatin Panama ba abu ne mai sauki ba.
Bayan haka, Julio Chur ya bayyana cewa, da ma dai a bayyane take cewa, kasar Panama tana dogaro kan hadin gwiwarta da wasu sauran kasashen duniya, wannan ne dalilin da ya sa kasar ke bi sannu a hankali, wajen raya dangantaka tsakaninta da Sin a cikin dogon lokaci.
Julio Chur ya kara da cewa, kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, ba ma kawai na da ma'ana sosai ga dangantakarsu ba, har ma zai yi babban tasiri ga nahiyar Latin Amurka baki daya. Wannan kuma ya samar da makoma mai kyau a gare su wajen raya hadin gwiwa a nan gaba, da sa kaimi ga kasar Panama, wajen bunkasa cinikayya, da kara samun yawan kudin shiga, da kuma raya kimiyya da fasaha yadda ya kamata, tare da taimakawa wajen neman samun karin 'yancin kai ba tare da fuskantar tsangwama ba. (Fatima Liu)