in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi shawarwari da mataimakiyar shugaban kasar Panama
2017-06-13 19:07:58 cri
A yau Talata ne ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari da mataimakiyar shugaban kasar Panama kana ministar harkokin wajen kasar Isabel de Saint Malo de Alvarado.

A yayin shawarwarin, Mr.Wang Yi ya ce, gwamnatin kasar Panama ta yanke shawarar amincewa da manufar Sin daya tak a duniya, inda ta katse huldar jakadanci da yankin Taiwan tare da kulla huldar jakadanci da kasar Sin, kuma ta dauki wannan mataki ne bisa la'akari da bunkasuwar kasar cikin dogon lokaci da kuma muradun al'ummar kasar. Yadda kasashen biyu suka kulla huldar jakadanci wani muhimmin mataki ne a kokarin da suke yi na samar da alheri ga al'ummarsu.

Isabel de Saint Malo de Alvarado daga nata bangaren ta ce, Panama za ta martaba manufar Sin daya tak a duniya, kuma ba za ta kara tuntubar yankin Taiwan ba. Panama tare da kasar Sin za su zama aminai na aminci, kuma za su habaka hadin gwiwarsu a fannonin siyasa da tattalin arziki da yawon shakatawa da zuba jari da ilmi da sauransu, tare kuma da sa kaimin hadin gwiwar kasashe masu tasowa.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China