Tauraron na BDS na sa ido ne kan ayyukan abubuwa kamar gas da ake amfani da shi a gida da lantarki da ruwa da kwalbatoci da kuma harkar sufuri.
Yayin wani taro da aka bude a jiya kan amfani da taurarin BeiDou, Sun Jiadong, shehun malami a kwalejin kimiyya ta kasar Sin, ya ce taurarin BeiDou na da dimbin amfani, don haka akwai bukatar kara inganta ayyukansa.
An yi amfani da taurarin BeiDou a kamfanin samar da gas na Beijing, inda aka gano wuraren da iskar gas ke zurarewa daga bututu.
Wani jami'in cibiyar samar da taurarin Ran Chengqi, ya ce idan aka bunkasa taurarin ta yadda zai yi amfani da intanet tare da samun ilimi irin na na'ura, to bukatarsa zai karu a masana'antu ta yadda za a rika amfani da shi a ababen hawa da jirage mara matuka da kuma mutum-mutumi.
Darajar tsarin taurarin dan Adam na BeiDou a tsakanin masana'antu ka iya kai wa yuan biliyan 240 kawo shekarar 2020. (Fa'iza Mustapha)