in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu karuwar cinikin motoci masu amfani da sabon makamashi a Sin
2017-06-13 09:46:18 cri

Wata kididdiga daga masana'antun kasar Sin ta nuna cewar, an samu bunkasuwa ta fuskar kerawa da kuma cinikin motocin dake amfani da sabon makamashi a kasar Sin a watan Mayu.

Jimillar motocin na NEVs dubu 45 ne aka yi cinikin su a watan Mayu, adadin da ya karu da kashi 28.4 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kana motocin na NEVs dubu 51 ne aka kera, adadin da ya karu da kashi 38.2 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, in ji wata kididdiga da kungiyar masana'antun kera motoci ta kasar Sin (CAAM) ta fitar a ranar Litinin.

Adadin cinikin motoci bai sauya ba, inda ya kai miliyan 2.1 a watan Mayu, adadin da ya karu da kashi digo 6 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan Afrilu, kan adadin da ya ragu da kashi digo 1 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Baki daya, an kera motocin da yawansu ya kai miliyan 2.09 a watan Mayu, adadin da ya ragu da kashi 2.4 bisa 100 idan aka kwatanta da watan Afrilu, kana adadin da ya karu da kashi digo 7 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China