Mista Thomsen ya ce, gwamnatin kasar Sin na nuna himma da kwazo, wajen shawo kan matsalar gurbacewar ruwan teku a halin yanzu, da kyautata wasu matakan da take dauka ta fuskar teku, lamarin da ya burge shi kwarai da gaske.
An gudanar da babban taro kan harkokin teku karo na farko na MDD a birnin New York a wannan mako, da zummar tabbatar da cimma daya daga cikin muhimman buri, na shirin neman ci gaba mai dorewa nan da shekara ta 2030, wato kiyayewa, gami da yin amfani da albarkatun ruwan teku cikin tsawon lokaci, ta yadda za'a samu ci gaba mai dorewa a harkokin tekun. (Murtala Zhang)